Home Labaran DuniyaTsohon sakataren gwamnatin Tarraya David Lawal Babachir ya fice daga jam’iyyar ADC

Tsohon sakataren gwamnatin Tarraya David Lawal Babachir ya fice daga jam’iyyar ADC

by KABIRU BASIRU FULATAN

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ya zargi shugabannin jam’iyyar da tafka magudi a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa domin bai wa Atiku Abubakar nasara.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Babachir ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne saboda abin da ya bayyana a matsayin “babban magudin da aka yi a dukkan matakan zaɓen fidda gwani” domin fifita Atiku.

Harin sama na haɗin gwiwar Najeriya da Amurka ya hallaka mayakan ISWAP 21 a Borno

Atiku ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC bayan ya kayar da Rotimi Amaechi da kuma Mohammed Hayatu-Deen. Sai dai duka biyun sun yi watsi da sakamakon zaɓen tun kafin a kammala tattara kuri’u.

Babachir ya ce ya lura da abin da ya kira “makircin yin shiru” kan abin da ya faru, yana mai cewa sakamakon zaɓen an rubuta ko kuma an sake rubuta shi ne domin bai wa Atiku da magoya bayansa nasara.

“Ko a wuraren da aka yi kamar an gudanar da zaɓe, an maye gurbin waɗanda suka yi nasara da mutanen ƙungiyarsa. A zahiri, abin kunya ne,” in ji shi.

Tsohon SGF ɗin ya bayyana cewa ba zai ci gaba da zama a jam’iyyar da yake zargin za ta iya amfani da irin waɗannan dabaru a babban zaɓen shekarar 2027 ba.

Ya kuma yi zargin cewa Atiku da na kusa da shi suna fifita muradun ƙabila da addini fiye da muradun ƙasa. A cewarsa, mara wa Atiku baya a zaɓen 2027 zai ba wa Bola Ahmed Tinubu damar samun tikitin wa’adi na biyu cikin sauƙi.

Babachir ya ce duk da rashin gamsuwarsa da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiya, yana ganin shugaban ƙasar na yanzu zai iya zama mafi alheri ga Najeriya idan aka kwatanta da Atiku.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da tuntuba da masu ra’ayi iri ɗaya da shi domin nemo hanyar hana Atiku kusantar kujerar shugaban ƙasa, kafin ya koma gonarsa domin ci gaba da harkokin noma.

Babachir Lawal ya fice daga jam’iyyar APC a watan Yunin bara bayan rashin jituwarsa da wasu manufofin jam’iyyar. A zaɓen 2023, ya ƙi goyon bayan Tinubu saboda zaɓin da APC ta yi na tsayar da Musulmi biyu tak a tak, bayan Tinubu ya zaɓi Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Ficewar Babachir daga ADC na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa ƙarfi domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, lamarin da ka iya ƙara haddasa rabuwar kai a cikin jam’iyyar.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 1   +   4   =