Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar rundunar sojin Amurka a Afirka, United States Africa Command, sun kashe mayakan kungiyar ISWAP 21 a wani harin sama da aka kai a yankin Arege da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno State.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa an kai harin ne ranar Asabar bayan bayanan sirri da sa ido sun tabbatar da kasancewar mayakan kungiyar a wani sansani da suke amfani da shi wajen shirya hare-hare a yankin Tafkin Chadi.
Majiyar tsaro ta bayyana cewa harin ya lalata sansanin tare da kashe mayaka 21, lamarin da ya raunana karfin ayyukan kungiyar ta ISWAP.
Rahoton ya ce farmakin wani bangare ne na ci gaba da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka domin tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda da hana su gudanar da hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.
Hukumomin soji sun ce nasarar aikin na nuna yadda haɗin kai tsakanin jami’an tsaron Najeriya da ƙasashen ƙawance ke ƙara ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci da inganta tsaro a yankin.
Wannan farmaki ya zo ne makonni kaɗan bayan wasu hare-haren sama na haɗin gwiwar Najeriya da Amurka da suka kashe sama da mayakan ISIS/ISWAP 20 a yankin Metele na jihar Borno.