Jami’ar Northwest Kano ta gabatar da sakamakon wani binciken lafiyar al’umma da ɗaliban fannin Likitanci (MBBS) suka gudanar a Unguwar Doka da ke Ƙaramar Hukumar Tofa a Jihar Kano. An gudanar da taron ne bayan kammala zangon aikin koyon aiki na uku na ɗaliban, inda aka bayyana cewa binciken zai taimaka wajen tsara manufofin kiwon lafiya da inganta ayyukan kula da lafiyar al’umma.
Da yake jawabi a madadin Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Amina Salihi Bayero, Bursar na jami’ar, Malam Salmanu Muhammad Kibiya, ya ce binciken ya nuna irin muhimmancin haɗin gwiwar jami’a da al’umma wajen samar da hujjojin da za su taimaka wa gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen ɗaukar matakan inganta harkokin lafiya. Ya kuma gode wa Hukumar Ƙaramar Hukumar Tofa da mazauna yankin bisa haɗin kan da suka bayar.
Shugaban taron kuma Provost na Kwalejin Kimiyyar Lafiya, Farfesa Aliyu Abdu, ya ce an mayar da binciken daga Ƙaramar Hukumar Shanono zuwa Tofa ne saboda matsalolin tsaro. Ya bayyana cewa shirin Community Diagnosis na bai wa ɗaliban likitanci damar fahimtar matsalolin kiwon lafiyar al’umma a aikace, tare da ba da shawarwarin hanyoyin magance su.
Rahoton binciken ya nuna cewa an tattara bayanai daga mutum 286 a ƙauyuka uku, inda aka mayar da hankali kan lafiyar mata da yara, cututtukan zuciya, yanayin zamantakewa da tsaftar muhalli. Sai dai ɗaliban sun ce sun fuskanci ƙalubale irin su ƙin amsa tambayoyi daga wasu mazauna yankin da kuma rashin tsarin gidaje, wanda ya ɗan kawo cikas wajen tattara bayanai.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Tofa, Alhaji Yakubu Ibrahim, ya ce majalisar za ta yi amfani da sakamakon binciken wajen inganta kiwon lafiyar al’umma. Shi ma Dagacin Doka, Alhaji Mustapha Mansur, da Shugaban Sashen Lafiya na ƙaramar hukumar, Alhaji Sani Abdu, sun yabawa jami’ar da ɗaliban bisa wannan bincike, tare da kira da a ci gaba da haɗin gwiwa domin amfanin al’umma.