Home LabaraiFCCPC ta gargaɗi dillalai kan tsadar fetur duk da faɗuwar farashin ɗanyen mai

FCCPC ta gargaɗi dillalai kan tsadar fetur duk da faɗuwar farashin ɗanyen mai

Hukumar ta ce za ta ci gaba da sanya ido domin ɗaukar mataki kan masu ƙara farashin man fetur.

by KABIRU BASIRU FULATAN

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki (FCCPC) ta nuna damuwa kan yadda farashin fetur bai sauka yadda ya kamata ba, duk da faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa za ta binciki masu kasuwancin mai idan aka samu shaidar cewa suna cutar da jama’a ta hanyar ci gaba da sayar da fetur da tsada ba tare da dalili ba.

Ƙungiyoyin Masu Buƙata ta Musamman Sun Nemi Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Hukumar A Jihar

Babban Jami’in Hukumar FCCPC, Tunji Bello, ya ce masu kasuwancin mai su kan ƙara farashin fetur da zarar farashin ɗanyen mai ya tashi, amma suna jinkirta rage farashin idan ya faɗi.

“Mun damu cewa yayin da masu kasuwancin mai ke gaggauta ƙara farashin fetur idan farashin ɗanyen mai ya tashi, suna ɗaukar lokaci mai tsawo kafin masu amfani su amfana idan farashin ya sauka,” in ji Bello.

Ya bayyana cewa duk da kasuwar fetur ce za ta ƙayyade farashi, amma FCCPC na da ikon haƙƙin masu amfani da kayayyaki.

Hukumar ta ce binciken da take yi ya nuna cewa an rage farashin fetur kaɗan ne duk da gagarumar faɗuwar farashin ɗanyen mai a duniya.

A yanzu haka, gidajen mai da dama na ci gaba da sayar da fetur kusan Naira 1,200 kan kowace lita.

“Idan muka samu sahihan hujjojin cewa ana cutar da masu amfani da kayayyaki ko ana karya dokoki, hukumar za ta gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace,” in ji Bello.

Hukumar ta kuma buƙaci ’yan Najeriya su riƙa kai rahoton ƙara farashi ko cin zarafin masu amfani da kayayyaki yayin da take ci gaba da sa ido kan kasuwar man fetur.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 9   +   2   =