Ƙungiyoyin masu buƙata ta musamman a Jihar Kano sun sake yin kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta aiwatar da dokar kafa tare da fara aikin Hukumar Masu Buƙata ta Musamman ta Jihar Kano, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen kare haƙƙoƙinsu da inganta walwalarsu.
Ƙungiyoyin sun bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, inda suka ce lokaci ya yi da za a fara aiki da hukumar domin ta cika manufofin da aka kafa ta a kai.
Sun ce fara aiki da hukumar zai samar da ingantaccen tsari na kula da harkokin masu buƙata ta musamman, daidaita shirye-shiryen gwamnati da suka shafe su, da kuma tabbatar da aiwatar da dokoki da manufofin da ke kare haƙƙoƙinsu.
A cewarsu, hukumar za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa damar ilimi, kiwon lafiya, horar da sana’o’i, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da cewa masu buƙata ta musamman sun samu cikakkiyar dama wajen shiga harkokin ci gaban jihar.
Yayin da suka yabawa Kwamishinan Ibrahim Abdullahi Waiya bisa yadda yake sauraron koke-kokensu da kuma bai wa kowa damar bayyana ra’ayinsa, ƙungiyoyin sun bukace shi da ya ci gaba da isar da buƙatunsu ga gwamnatin jihar domin ganin an gaggauta fara aikin hukumar.
Sun bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki matakin da ya dace wajen tabbatar da fara aikin Hukumar Masu Buƙata ta Musamman, domin inganta rayuwar wannan ɓangare na al’umma da kuma tabbatar da cikakken shigarsu cikin harkokin ci gaban Jihar Kano.